Masar Ba Zata Kyale Masu Sa Ido Na Kasa Da Kasa A Zaben Kasar Mai Zuwa Ba

Masu zanga zanga suka hallara a dandalin Tahrir dake Alkahira.

An bada rahoton cewa wani jami’in Majalisar mulkin soja ta kasar Masar Janaral Mamdouh Shaheen ya fada a jiya laraba cewa, ba za’a bari masu lura na kasashen waje su nazarci zaben bayan juyin juya hali da za’a yi ba.

Kamfanin dilancin labarun Associated Press ya ambaci Janaral Mamdouh Shaheen yana fadin cewa hana masu lura na kasa da kasa nazarin zaben ya zama dole domin kare diyaucin Masar, ya kara da cewa ba wani abu suke boyewa ba.

To amma an ambaci wani dan kishin kasa mai suna Hafez Abou Saad yana fadin cewa da walakin, goro cikin miya, domin alkawarun da soja suka yi cewa za’a gudanar da zaben cikin yanci da adalci basu wadatar ba, kuma hana masu lura na kasa da kasa suyi nazarin zaben, ya sa ana tababar gaskiyar gudanar da zaben babu kumbiya kumbiya.