Masu kada kuri’a a kasar Sao Tome and Principe zasu zabi sabon shugaban kasa yau Lahadi. Yan takara goma suke fafatawa domin gadon shugaba Fradique Menezes wanda kundin tsarin mulkin kasar ya haramtawa neman wa’adin mulki na uku. Yan takarar sun hada da tsohon shugaban kasar Manuel Pinto da Coasta, wanda ya yi mulki na jam’iya daya karkashin jam’iyar ‘yan gurguzu tsakanin shekara ta dubu da dari tara da saba’in da biyar zuwa dubu da dari tara da casa’in. da kuma tsohon PM Evaristo de Carvalho. Sabon shugaban kasar zai fuskanci kalubalar fidda kasar daga kangin talauci da ya yi mata katutu. An hakikanta cewa, Kasar dake tsibirin mashigin tekun Guinea, tana da arzikin man fetir tana kuma iya fice a fannin harkokin yawon bude ido. Mutane dubu casa’in da biyu ne aka yiwa rajista domin kada kuri’a. Yana yiwuwa a sami sakamakon zaben yau da dare. Za a gudanar da zaben fidda gwani a cikin wannan watan idan babu dan takarar da ya sami rinjaye.