Daruruwan yan kasar Tunisia sunyi gangami a Tunis, baban birnin kasar domin yin Allah wadai da tarzoma da kuma rudamin data dabaibaiye kasar, bayan da aka yi zanga zangar cikin 'yan kwanaki da suka shige, harma aka kashe wani yaro dan shekara goma sha hudu da haihuwa.
Kusan jam'iyun siyasa goma sha biyu suka shirya jerin gwanon ta ranar Alhamis suna kira da'a gudanar da shirin kafa mulkin democradiya cikin lumana.
Wannan gangamn bata hada da wata jam'iyar Islama, da aka dauka kungiyar ce ta masu ra'ayin sausauci ba, to amma kuma wasu suna zarginta da laifin ruruta wutar rikici a kasar. Ita dai wannan kungiya ko jam'iya ta musunta cewa ta taka rawa a tarzomar da aka yi a kasar a kwanan nan
Wasu 'yan kasar Tunisia sun baiyana tsoron cewa arangamomin da ake yi, zasu dakushe begensu ta ganin an kafa mulkin democradiya a kasar.
Daruruwan yan kasar Tunisia sunyi gagami a Tunis baban birnin kasar, domin yin Alah wadai da tarzoma da kuma rudami, bayan da aka yi zanga zangar a 'yan kwanaki da ska shige harma aka kashe wani yaro dan shekara goma sha hudu da haihuwa.