Masanan Lafiya Sun Kiyaye Ranar Cutar Ciwon Hakarkari ta Duniya

Wasu 'yan yara masu fama da cutar ciwon hakarkari

A duniya baki daya, fiye da yara miliyan guda yan kasa da shekara biyar ne ke mutuwa a kowacce shekara.
Kowacce shekara, fiye da yara miliyan daya ne suke mutuwa daga cutar ciwon hakarkari. Wannan na cikin babbar cuta mai kashe yara yan kasa da shekara biyar a duk fadin duniya. Ranar wannan cutar ta duniya (11/12), masanan lafiya suka ce ko yake hanyoyin kare wannan ba su da yawa, amma akwai ingantattun hanyoyi kadan da zasu taimaka wajen kiyaye irin wannan mutuwar. Taken wannan shekara na ranar cutar ciwon hakarkari shine “Sabuwar al’ada ta kauda cutar hakarkari ta yara.”

Ciwon hakarkari ya shafi sashin huhu don haka iskar da kake shaka, bata iya shiga cikin hanyar jini. Don haka lumfashi yake zamar wa yaro da wuya, wannan shi kai yaro kamuwa da cutar. Irin cutar hakarkarin da take kashewa ita ce wadda ta samu tawurin kwayar bakteriya, koda yake akwai na irin cutar kwayar virus.

A duniya baki daya, fiye da yara miliyan guda yan kasa da shekara biyar ne ke mutuwa a kowacce shekara. Ainihin yawan yaran dake kamuwa da cutar sun ninka masu mutuwa har wajen sau goma. Don haka, yara wajen biliyan daya ne suke kamuwa da ciwon hakarkari, amma wadansu suna samun magungunan da suke bukata.

Yawancin mutuwa ta wannan cuta na samuwa ne a kasashe masu tasowa inda samun magani na da wuya. Yara sun fi kamuwa da cutar ne lokacin suna kanana. Rashin isashshen abinci ko kuma kamuwa da kwayar cutar kanjamau, suna iya kara yawan yaran dake mutuwa.

Babban masanin lafiya a Asusun tallafawa yara, Dr. Mark Young, yace za’a iya kiyaye yawancin mutuwar yara daga ciwon hakarkari. Yace akan matsayin kariya, idan yaro ya sami abinci mai nagari, ya sha nono kawai, idan suka sami ruwan sha mai kyau da tsabta da wankin hannu – irin wadannan abubuwan suna kare yara daga kamuwa da cutar a mataki na farko. Hakanan kuma za’a iya yin amfani da allurar rigakafi mai inganci domin samun kariya.

Kuma idan yaro ya kamu da kwayar cutar ciwon hakarkari. Dr, Young yace, ana iya maganinsa da wuri. Akwai magunguna masu inganci masu kuma saukin sha ga yara kamarsu amoxicillin, wadanda suke aiki sosai a cikin yara. Wani abu mai wuya shine gane cutar daga iyaye da wuri. Zasu gane ta wurin ganin yaro mai tari ko wahalar lumfashi. Iyali na bukatar gane wannan kamin daukar mataki na yin magani.

Kasashe da yawa suna inganta samun maganin ciwon hakarkari, da kuma wadansu cututtuka kamar su gudawa, wata cutar da ta ke yawan kashe yara kanana.

Hakanan kuma kungiyar GAVI, dake taimako wajen kara allurar rigakafi, tace tana taimakon fiye da kasashe 50 domin samun allurar rigakafin cutar hakarkari ya zuwa 2015.