An bayanna cewa ma’aikatan hukumomi suna bi gida gida suna gargadin dokokin kiwon lafiya.
Mutanen Namu, yayinda suke yin farin cikin samun saukin yaduwar cutar kwalara a garin sun nuna damuwa game da yawan masu zuwa Namu daga jihar Nassarawa domin zama.
Wani mutumin Namu, Mohammed Iliyasu, yace, “Babar matsalar da muke fuskanta ita ce mutum zaka bar gidanka ka je ka zauna a wani wuri daban? Wanan babar matsala ce.”
Inji wani malami mai suna Adamu Ivenya, “Har yanzu ina nan a Namu, kuma inda zanje in sa kai na da iyali na babu shi. Gwamnati ta taimaka tayi mana abin da za su iya domin mu koma gida, musaman inda zamu sa kan mu.”
Dr. Raymond Juryit, likita mai kula da cututuka masu yaduwa a jihar Plato ya ce ya kamata mutane su lura kuma su bi dokokin da aka bayar domin kiyayewa daga cutar kwalara.
Zainab Babaji ce ta aiko da rahoton daga Jos.