Kafin daukar wanan matakin bada rigakafin cutar sankarau da gwamnatin Najeriya ta bada umurni ayi, an samu wadanda suka fara kamuwa da cutar a jihar Naija kuma mutum guda ya rasa ranshi.
Wani direktan ma’aikatar lafiya a jihar Naija, Dr. Iya Bage Aliyu, ya yi bayani cewa mutum daya ne kawai ya rasa rai daga cikin mutane shida da suka kamu da cutar sankarau a jihar. Ya kuma ce gwamnatin tarraya ce ta dauki matakin gudanar da allurar rigakafin, ba jihar Naija ba ce. Ya kuma ce, “Ana yin gangamin ne a wuraren da ake kira meningitis belt, inda ake yawan samun sankarau.”
Dr. Aliyu ya ce, babu fargabam sake barkewar sankarau a jihar. Ya fadi cewa alurar da suka bayar zata kiyaye jama’an da suka karbi rigakafin har zuwa shekara goma.
Wakilin Sashen Hausa Mustafa Nasiru Batsari ya aiko da rahoton.