A sanarwar da ta bayar ta hanyar kafafen gwamnatin kasar, Faransa ta bayyana labarin kisan Soumana Boura, dan Nijer da ke shugabancin reshen kungiyar IS a yankin Sahara wato EIGS ranar Talata, wanda ya hadu da ajalinsa a wata malabar ‘yan ta’adda da ke arewacin jihar Tilabery sakamakon wani farmakin sama da aka kai a ranar Litinin. Tuni masana suka fara bayyana matsayinsu dangane da wannan al’amari.
Dr. Abba Sidik masani ne akan sha’anin tsaro, ya ce ‘yan IS sun sanya ‘yan Nijer da yawa cikin kungiyar don su taimaka musu, wanda aka kashe ya na cikin irinsu kuma kisan shi tamkar wani sakon kashedi ne ga manyan kungiyar.
Gudummowar dakarun tsaron Nijer ta taimaka wajen rutsawa da wannan kasurgumin dan ta’addan da ya addabi al’umomin garuruwan da ke kan iyakokin kasashe 3 wanda kuma aka bayyana a matsayin wanda ya jagoranci kisan Faransawa 6 da ‘yan rakiyarsu 2 a gandun dajin Koure mai tazarar kilomita 60 da birnin Yamai a watan Agustan 2020, a cewar hukumomin faransa.
A ra’ayin Moustapha Abdoulaye da ke sharhi akan harakokin tsaro, dauko yaki daga tushe shine mafi a’ala a maimakon kisan dauki dai dai. Ya kuma ce wannan ba aikin Faransa bane kadai, kowa na da hakkin taimakawa.
Ko da yake ana kallon kisan Soumana Boura a matsayin wani matakin shan fansar kisan Faransawa da ake dora alhakin a wuyansa, Editan jaridar La Roue de l’histoire Ibrahim Moussa, na yi wa abin wata fahimta ta daban. Ya na mai cewa Faransa ba ta fitowa ta ce ta kashe wani gagarumin dan ‘ta’adda sai jama’a sun nuna kyamar kasancewar sojojin Faransar a kasar. A ganinsa wannan wata dabara ce ta a mance da zanga-zangar da ake yi.
Kafin dubunsa ta cika, Soumana Boura na shugabancin wata runduna mai kunshe da gomman mayakan jihadi wadanda ke aika-aika a karkarar Gober Gourou da Firo da ke yankin yammacin Nijer. Ana masa kallon na hannun daman Abou Walid Alsaharoui wanda a bisa umurninsa ne suka kashe wadannan Faransawa na kungiyar agaji ta ONG ACTED.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5