Bullar cutar murar Korona, a iya cewa ta girgiza fannin kiwon lafiya na kasashen duniya baki daya.
Wannan ne yasa kasashe masu karfi a duniya suka ta yin kokari ganin sun fito da allurar rigakafin cutar a yayinda suka bar kasashe marasa karfi a baya.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dr. Bashir Bello babban jami'in a fannin gudanarda bincike-bincike a jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato ya ce akwai wasu cuttuka kamar zazzabin Lassa da ke tare da mu a Najeriya da wasu kasashe a Afirka ta yamma da har yanzu ba 'a samu maginsu su ba, bayan shekaru 50 da bullarsu, domin ana jira turawa su samar da magani ko rigakafi, amma ba 'a san yaushe za su samo maganin ba.
Hakan ne ya zaburar da masana a Najeriya suma su yi amfani da ilimin su domin ganin sun bi sawun manyan kasashen da suka samar da maganin rigakafin.
Masana a Najeriya dai sunyi amannar cewa nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samar da magungunan rigakafin cutar ta murar Korona a cewar Abdullahi Abbas Yahaya, mukaddashin shugaban kwamitin kula da cututuka masu yaduwa a jami'ar Usmanu Danfodiyo.
who-na-tuna-zagoyawar-barkewar-cutar-covid-
afurka-ta-ce-ta-zaburo-kan-batun-rigakafin-cutar-corona
Masana fiye da 200 da suka tattauna akan wannan batun sun lura da kalubalen da ke tarnaki ga kasashe masu tasowa wajen samar da rigakafin cututuka dake addabar al’ummomin su da duka hada da rashin isassun kudi, da rashin samun kulawar gwamnatoci wajen ganin an samu nasarar samar da magungunan.
Wannan dai ba shine karon farko da masana a Najeriya ke kokarin samar da magungunan cututuka musamman ta korona ba, domin a watan Agusta na shekara ta 2020 ma an samu maganin da ake ganin cewa zai iya wakar da cutar daga Sakkwato amma bayan da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta karbi maganin don gudanar da bincike har yanzu shuru ake ji.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5