Binciken hukumar lafiya ta duniya ya tabbatar da cewa akwai akalla cututtuka 500 wadanda ke kama jama'a kuma akwai tabbacin cewa daga dabbobi ne suka samo asali.
Wannan a cewar likitoci wasu lokuta akan samu jama'a da wata cuta ayi ta bincike da shan magunguna amma a kasa shawo kan cutar.
Akan hakan ne likitocin ke ganin ya kamata Najeriya ta tafi tare da sauran kasashe a wannan haujin.
Bisa ga lura da cewa ba da jimawa ba ne hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta bayar da bayanin sake bullar cutar murar tsuntsaye a wasu jihohi a daidai lokacin da ake cikin murar mashako ga kuma yawan amfani da shan kayan sanyi da jama'a ke yi musamman masu azumi wanda hakan kan kawo kamuwa da mura ko ya likitocin mutane ke ganin wannan batun na binciken lafiya na hadin guiwa?
Kasancewar akwai cututtuka na mutane da dabbobi masu nuna alamu iri daya likitocin ke shawarar jama'a da kada a rika saurin daukar matakai da zaran an lura da alamar wata cuta domin saurin samu mafita ga matsalar.
Saurare cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5