Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Su Ka Sa Za Mu Shiga Yajin Aiki – Likitocin Najeriya


Wani likita yayin da yake duba wani mara lafiya a asibiti
Wani likita yayin da yake duba wani mara lafiya a asibiti

Kungiyar Likitocin Najeriya ta (NARD,) ta yi barazanar tsunduma yajin aiki na gama-gari a ranar Alhamis mai zuwa muddin gwamnati ba ta cika mata alkawaran da ta yi ba.

Wata sanarwa da ta fitar a karshen taronta na kasa da ta yi a karshen makon da ya gabata, kungiyar ta ce bukatun da suke nema gwamnati ta biya musu, sun hada da biyan su dukkan kudaden albashinsu da suke bi bashi ciki har da na watan Maris.

Najeriya dai na da likitoci akalla dubu 42, wadanda dubu 16 daga cikinsu ke kan horo na kwarewa.

Baya ga batun albashi, likitocin sun sha yin korafi kan rashin kayan aiki a asibitocin kasar kama daga abin da ya shafi gadaje zuwa magunguna

Kungiyar wacce ta ba da wannan sanarwa da amincewar jagororinta da suka hada da Sakataren yada labarai, Dr. Dotun Osikoya, ta ce ta ba gwamnatin wa’adin zuwa ranar 31 ga watan nan na Maris don a biya mata wadannan bukatu, in ba haka ba kuma, za ta shiga yajin aiki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Likitocin sun ce suna son a biya mambobin nasu da ke aiki a matakan asibitocin horarwa na tarayya da na jihohin.

Ga wasu daga cikin sauran bukatun da likitocin s uke nema a biya musu:

  • A karawa dukkan ma’aikatan kiwon lafiya kudaden da ake biyansu na saka kansu cikin hadari da kashi 50
  • A biya su alawus-alawus na kwadaitar da su yin aikin yaji da COVID-19 musamman a jihohi.
  • A sallami babban mai yin rijista na kungiyar likitocin hakora na Najeriya saboda gazawa da ake zargin ya yi wajen tura likitoci wuraren da za su yi aiki.
  • A biya su ragowar kudaden alawus da suke bi bashi na aikin zaman samun horo na shekarar 2019/2020
  • Samar da inshorar rayuwa

Yajin aikin likitoci dai ba bakon abu ba ne a Najeriya, a watan Satumbar bara likitocin suka koma bakin aiki bayan kwashe wani lokaci suna neman a biya musu wadannan bukato.

Ma’aikatan lafiya ma da suke yaki da annobar COVID-19 sun shiga yajin aikin na bayan nan abin da ya shafi ayyukan yaki da annobar.

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta CDC a kasar, ta yi kiysain cewa kusan likitoci dubu daya sun harbu da cutar COVID-19 a lokacin wancan yajin aiki.

XS
SM
MD
LG