ABUJA, NIGERIA - Liz Truss wacce tsohuwar sakatariyar wajen Burtaniya ce ta zama sabuwar Firai Ministar kasar bayan zaben ta a matsayin shugabar jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya wato Conservatives.
Truss dai ta gaji mukami daga tsohon Firai Minista Boris Johnson wanda ya fuskanci juya baya hatta daga jami’an gwamnatin sa in ka debe irin Truss din da ta bi a hankali har faduwar gwamnatin.
Masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Abuja Dr. Farouk BB Farouk ya ce Truss za ta iya fuskantar turjiya daga masu matukar hamaiya da manufofin ko-in-kula na Johnson da kuma ba ta yi adawa da hakan ba.
Kazalika Dr.Farouk ya nuna matsalar tattalin arziki da ta sa lalle mutane na bukatar tallafi ka iya zama wata babbar damuwa don Truss ta ki amincewa da karin haraji don daidaita tattalin arzikin kamar yadda wanda ta kayar a zaben, Rishi Sunak ke fatar aiwatarwa.
A nan Dr.Farouk ya ce sai Truss ta jajirce kafin madafun iko su zauna dam a hannun ta “akwai gungun masu adawa da tsarin Boris Johnson wanda zai iya ci gaba da tasiri a cikin mulkin ta.”
Liz Truss da a ka haifa a shekarar 1975 ta zama mace ta uku da ta zama Firai Ministar Burtaniya bayan Margaret Thatcher da Theresa May.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5