ABUJA, NIGERIA -Bayan shafe makonni shida a hannun hukumar tsaron cikin gida ta DSS, babbar kotun Tarayya da ke zama a yankin Ikoyi na jihar Legas, ta ba da belin dakataccen gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele a kan kudi Naira miliyan 20.
Babbar kotun Tarayyar karkashin jagorancin mai shari’a Nicholas Oweibo ce ta ba da belin na Emefiele tare da umarnin a tsare shi a gidan yari na Ikoyi har sai an kammala cika sharuddan belinsa.
Sharuddan sun hada da samar da mutum guda da shi ma zai ba da Naira miliyan 20 da karbe fasfo dinsa.
Mai shari’a Nicholas Oweibo ya bayar da belin Emefiele ne bayan ya isa babbar kotun Tarayya da misalin kare 9 da wasu mintuna inda aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhumar shi da laifuka biyu da suka hada da mallakar bindigogi da alburusai ba bisa ka’ida ba bayan ya saurari shawarwarin lauyan Emefiele, Joseph Daudu mai makamin SAN.
A yayin zaman kotun dai, alkalin ya yi watsi da ikirarin Gwamnatin Tarayya daga bakin lauyanta na cewa akwai yiyuwar Emefiele ya arce a kasa ta jirgin sama tare da yanke hukuncin cewa gwamnati ta gaza samar da wata hujjar da za ta goyi bayan ikirarinta.
Tuni dai masu bibiyan al’amurran yau da kullum da kwararru a sha'anin siyasa da shari’a suka fara yin tsokaci a kan wannan batu.
Mai sharhi a kan siyasa da sauran al’amurran yau da kullum kuma Shugaban kamfanin kasuwanci da zuba jari na kasa da kasa, GITC , Malam Baba Yusuf, ya ce ba da belin Godwin Emefiele bai zo da mamaki ba ganin irin take-taken da aka yi ta gani a cikin makonnin uku zuwa hudu da suka gabata.
“Amma mu sani akwai wasu laififfukan kuma da ake tuhumar shi akai, maganar yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a aikinsa a nan babban bankin da daukar ma’aikata ba bisa ka’ida ba da sauran su”
Shi ma Malam Aminu Abbas Gumel ya bayyana cewa “Idan dai za mu iya tunawa watan da ya wuce tsohon gwamnan babban banki wato Godwin Emefiele an kama shi ne a bisa wasu dalilai wadanda sun kai guda biyar ko shida. A cikin su dai na san akwai abin da ake kira “bridge of trust” akwai ta’addanci, akwai kokarin ta da tarzoma, da kuma almundahana da kudadde, to yau sai muka wayi gari da labarin an kai shi kotu a bisa zargi guda biyu wanda ya hada da mallakar bindiga da kuma harsashai, an kuma ba da belinsa.
Ya kara da cewa, "amma wannan ba abu ne na ta da jijiyon wuya ba, za mu jira mu ji shin wadandan laifuffuka da ake zargin sa da su, su kadai ne, sauran an wanke shi, ko kuma akwai ranar da za a sake kai shi kotu a bisa wadancen zarge-zargen da ake masa.”
A bangare tanade-tanaden doka, fitaccen masanin kundin tsarin mulkin Najeriya, Barrister Mainasara Kogo, ya ce bada belin Godwin Emefiele bai zo da mamaki ba saboda talasurancin dake tattare da tsarin shari’ar kasar yana mai cewa muddin ba’a yiwa sashe na 36 da sashe na 230 zuwa na 304 gyara ba, zai kasance duk wani wanda ke da laifi shine zai rika morewa tsare-tsaren shari’ar da Najeriya ke da su.
Idan ana iya tunawa, shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya ne a ranar 9 ga watan Yunin shekarar 2023 kuma kwana daya tak da dakatar da shi hukumar tsaro ta DSS ta tabbatar da kama shi.
A irin wannan yanayi dai, masana na jadada mahimmancin bukatar bin dokokin kula da haƙƙin ɗan adam na ƙasa da ƙasa cewa yin shari'a na gaskiya na dogara ne akan bincike na gaskiya da rashin son kai a bisa cikakken bin ƙa'idodin doka da haƙƙin ɗan adam a bangarorin gwamnati, wadanda ake zargi da aikata laifuffuka da saura masu ruwa da tsaki don yin adalci.
Saurari ciakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5