Masu bincike a Canada sun yi amfani da wata kwayar cuta da aka yi wa kwas-kwarima wajen yaki da cutar sankara. Kwayar cutar zata yaki sankarar ba tareda tayi illa ga sauran naman jikin Bil’adama ba.
Masu bincike a Canada sun yi amfani da wata kwayar cuta da aka yi wa kwas-kwarima wajen yaki da cutar sankara. Kwayar cutar zata yaki sankarar ba tareda tayi illa ga sauran naman jikin Bil’adama ba.
Masana kimiyya sun juma suna nuna sha’awar amfani da wan nan hanya wajen yaki da cutar sankara ko kansa. An samu karin sha’awar a baya bayan nan, musamman ma da kara gano hanyoyin kimiyya na gina halittu ko sake yanayinsu, wadanda suka baiwa kwararru damar gina kwayoyin cuta da zasu iya auna wurare da cutar sankara ta kama a jikin Bil’adama.