Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Woyar Amurka Tana Dab Da Durkushewa idan ba....


US Postal Service mailboxes are seen awaiting disposal September 1, 2011, in San Jose, California.
US Postal Service mailboxes are seen awaiting disposal September 1, 2011, in San Jose, California.

Shugaban hukumar woya na Amurka, da aka fi sani da sunan Postmaster General, Patrcik Donahue, yana gargadin cewa hukumar zata durkushe badi, idan majalisar dokokin Amurka bata bata izinin garambawul ga tsarin aikinta ba.

Shugaban hukumar woya na Amurka, da aka fi sani da sunan Postmaster General, Patrcik Donahue, yana gargadin cewa hukumar zata durkushe badi, idan majalisar dokokin Amurka bata bata izinin garambawul ga tsarin aikinta ba.

Donahue ya gayawa wani kwamitin majalisar dattijai cewa hukumar tana dab da durkushewa.Yace akwai bukatar a dauki wani mataki zuwa karshen watan nan, idan ba haka ba hukumar zata gaza kan inshoran kiwon lafiya na tsoffin ma’aikata da suka yi ritaya, da suka kai dala milyan dubu biyar da rabi.

Donahoe yace baya neman wani tallafi daga gwamnati, abinda yake bukata shine izini daga majalisar dokoki na yin sauye sauye kan yadda cibiyar take tafiyarda ayyukanta. Cikin matakan tsimin kudi da hukumar take son dauka sun hada da rufe wasu rassa dake cin kudi, haka kuma hukumar zata daina raba wasiku ranar Asabar.

Cibiyar gidan woya ta Amurka bata samun kudi daga baitulmalin gwamnati. Cibiyar reshen gwamnatin tarayya ce mai cin gashin kai.

Cibiyar tana hasarar dubban miliyoyin dala sabo da dumbin mutane sun koma amfani da email wajen aikewa da sakonini da wasiku.

Duk da haka cibiyar tana aikewa da sakonni da wasiku milyan dubu dari biyar ako wani wuni. An kafa cibiyar tun kamin Amurka ta sami ‘yancin kai. Benjamin Franklin ne shugaban hukumar na farko.

Jiya Talata, Senata Joseph Lieberman yace hukumar gidan woyar ba wani tsofon yayi daga karni na 18 bane, amma kadara ce ta karni na 21.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG