Daga watan Yuli zuwa yanzu an samu hare-haren kunar bakin wake 22 a jihar Borno wadanda suka yi sanadiyar mutane 292. A jihar Adamawa kuma an samu hare-hare hudu da suma suka lakume mutane da dama.
Hukumomin tsaron jihar Adamawa sun gana da shugabannin masallatai da mijami'u domin cimma matsaya akan tunkarar ta'adanci.
Malam Yusuf Usama na kungiyar agaji ta IZALA yace dole zasu dauki matakai a masallatai kana ya kira jama'a da su bada hadin kai domin a shawo kan ta'adanci. Yace daya cikin matakan da zasi dauka shi ne fitowar 'yan agaji da wuri har ma idan ta kama suna iya kwana a masallatan.
Ya kira jama'a da su daina taruwa a tsaye suna surutu maimakon su samu wuri su zauna su saurari hudubar limami.
Shi ma limamin sabon masallacin Juma'a da aka kaiwa harin kunar bakin waken ya roki jama'a kada a karaya amma a jajirce a hada kai da jami'an tsaro. Yace duka masallatai za'a kara matakan tsaro saboda kawar da bala'in ta'adanci. Ya kira jama'a su jajirce su bautawa Mahalicinsu. Idan lokacin mutuwa ya yi Alla na iya karban ran mutum koina yake.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5