Maryam Bambale : Za Mu Koyawa Matan Arewa Sana'o'i

Maryam Aliyu Bambale wata matashiya mai kishin yadda 'yan arewa ke tafiya ba tare da wani kwararan sana’o’in dogaro da kai ba, akan haka ne ma suka kaddamar da wani taron Northern Youth Summit.

An gudanar da taron ne dai domin a canza tunanin 'yan arewa, musamman matan yankin arewa wajen zama masu dogaro da kai, tare da kauracewa wannan tunanin na jiran komai sai gwamnati ta zo ta yi wa al’ummarta.

Malama Maryam ta ce wannan taro shine irinsa na farko da aka shirya domin zaburar da ‘yan arewa, kuma an shirya shine saboda yadda aka bar matan yankin na arewa, sabanin yadda matan yankin kudu ke tallafawa junansu ta hanyar janyo na kasa da su suna koya musu sana’o’in hannun domin su zamo masu dogaro da kai.

Sai dai kuma ta kara da cewa akan haka ne suka fito da wannan taron bita da zumar gina wasu wuraren da za’a koyawa wadanna matan sana’o’i, kuma za’a yi hakan, da kuma biyan wani abun hasafi domin samar da waje na koyon sana’a.

Sannan ita shugabar wannan tafiya ta ce sun tsara shirin ne na shekaru 16 masu zuwa da zummar tabbatar da an samar da canji mai dorewa.

Ta ce zasu koyar da mata sana’o’in kamar su dinki, ko aikin kafinta da takalma da jakkuna da dai sauransu.

Sannan Marya ta ce dole ne su tashi tsaye ko da gwamnati ta taimaka musu ko akasin haka, za su samar da wata hanyar da za su tara kudaden daga wajen al’umma domin tabbatar da wannan kudiri na su ya tabbata.

Your browser doesn’t support HTML5

Maryam Bambale : Za Mu Koyawa Matan Arewa Sana'o'i