Mario Mandzukic Ya Yi Murabus Daga Taka Leda A Matakin Kasa Da Kasa

Shararren dan wasan kwallon kafa dake taka leda a kungiyar Juventus dan kasar Croatia, Mario Mandzukic, ya sanar da murabus daga kwallon kafa ta kasa da kasa.

Dan wasan mai shekaru 32 da haihuwa ya kasance daya daga cikin 'yan wasan Croatia da suka kai ga wasan karshe na gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihin kasar Croatia, wasan da ya gudana a shekarar 2018 a kasar Rasha.

Mandzukic, ya buga wa kasar Croatia wasanni har guda 89 tun daga lokacin da ya fara bugawa mata a shekarar 2007. ya samu nasarar zurara kwallaye har guda 33.

Kuma shine ya jefa wa kasar sa kwallon da ta basu nasarar kaiwa wasan karshe a gasar ta cin kofin duniya na bana da aka gudanar a kasar Rasha, tsakaninsu da kasar Ingila a wasan daf da karshe da aka tashi Croatia nada ci 2 da 1.

Sai dai a wasan karshe kasar faransa ta lallasa Croatia, da kwallaye 4 da biyu wanda hakan ya sa kasar Croatia tazo na biyu a gasar da lambar Azurfa.

Dan wasan Mandzukic, yanzu haka yana buga wa tawagar ‘yan wasan Juventus da ke kasar Italiya tun daga shekarar 2015.

Your browser doesn’t support HTML5

Mario Mandzukic Ya Yi Murabus Daga Taka Leda A Matakin Kasa Da Kasa