Yayinda ake shirye shiryen rufe saye da sayarwar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya musamman a Nahiyar kasashen Turai wanda suka hada da kasar Spain, Italiya, Faransa da kuma kasar Jamus, a karshen watan Agustan wannan shekarar.
Kungiyoyin kwallon kafa da dama sun dukufa wajan ganin sun kammala sayen ‘yan wasan da suke bukata domin fafatawa a kulob din su musamman akan wasan su na kakar wasannin bana.
Kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain dake kasar faransa na shirin bada zunzurutun kudi har fan miliyan 100 don sayen dan wasan Dan wasan Tottenham mai shekaru 26 mai suna Christian Eriksen. Har ila yau kungiyar ta PSG tana sha'awar dauko dan Tottenham, dan kasar Ingila Danny Rose, inda kungiyar ta Tottenham, take son sayar da dan wasan mai shekaru 28 da haihuwa a wannan watan kafin rufe kasuwar hada hadar.
Shi kuwa Shugaban kungiyar kwallon kafa na Barcelona, Joseph Maria Bartomeu, ya ce bai cire tsammani wajan sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Manchester United dan kasar Faransa Paul Pogba, ba mai shekaru 25, da haihuwa kuma ya ce "har yanzu akwai sauran lokaci don yin kasuwanci" a cikin rani na canja sheka.
Sabon Kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Julen Lopetegui, ya ce yana da bukatar sayen ‘yan wasa a kulob din wadanda suka hada da mai tsaron Baya a kungiyar da kuma dan wasan gaba kafin a rufe cinikayyar ‘yan wasa a karshen watan nan.
Facebook Forum