Dan wasan Kwallon Badminton a turance mai suna Ahmed Balarabe Umar wanda ya wakilci Najeriya a gasar wasannin motsa jiki na Matasan Afrika, (All African Youth Game) da ya gudana a kasar Algeriya 2018 cikin watan Yuli ya samu gagarumar nasara.
Ahmed, mai shekaru 16 da haihuwa dan asalin jihar Bauchi, a tarayyar Najeriya, ya samu nasarar lashe lambobin yabo har guda hudu, wadanda suka hada da Zinare 2 Azurfa 1 Tagulla 1 acikin wasanni hudu daban daban bangaren badminton da ya buga a yayin da yake wakiltar tarayyar Najeriya a can kasar Aljeriya.
Wasannin da ya buga sun hada da (Team Event ya samu Goal Medal)
(Doubles Event Goal Medal)
(Mix Doubles Silver)
sai kuma
(Single Event Bronze)
Ya kuma buga wasaninne da kasashe daban daban wadanda suka hada da Moroshiya, Algeriya, Masar, Buswana. A wasan karshe kuwa ya buga da takwaransa na Najeriya, ne mai suna Daniel Christoph, da kuma BabaTunde Bankule, inda ya shasu 2-1.
Wannan nasara da Ahmed, ya samu ta bashi damar zuwa wakiltar Najeriya a bangaren badminton, a wasannin motsa jiki na matasa na duniya wato (Youth Olympic) wanda za a yi a watan Oktoba 2018 can kasar Ajantina.
Bayan dawowarsa daga kasar Algeriya, wakilin dandalinvoa.com a jihar Bauchi ya zanta da dan wasan kan ko akwai abunda gwamnatin tarayya ko kuma ta jiharsa ta masa na wani muhimmiyar kyauta ganin cewa ya samo wa kasarsa lambar yabo, sai a zuwa yanzu dai babu wani abu amma dai gwamnatotin na ta shirye shirye domin masa wata kyauta ta musamman.
Bayan haka ya yaba wa kungiyarsa ta Uban Dawaki Badminton Club, dake Bauchi da kuma Alhaji Abdul Ilelah, Uban Dawakin Bauchi, da sauran manya manyan mutane bisa irin tallafa masa da suke yi wajan al’amuransa
Saurari kuma hirar Bala Branco yayi da Ahmed a nan.
Facebook Forum