'Yan Kunar Bakin Wake Sun Hallaka 'Yan Shia da dama a Iran

Wata motar daukar majinyaci a wurin da aka kai harin bam a Iran a garin Chahbahar da ke Iran, ran 15 Dis. 2010

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wani taron addini na ‘yan Shi’a, sun jijjiga birnin Chahbahar na kusancin kadsar Iran, inda mutane 39 a kalla su ka rasa rayukan su, wasu kuma fiye da 90 su ka ji ciwo.

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wani taron addini na ‘yan Shi’a, sun jijjiga birnin Chahbahar na kusancin kadsar Iran, inda mutane 39 a kalla su ka rasa rayukan su, wasu kuma fiye da 90 su ka ji ciwo.

Gidan talbijin din gwamnatin kasar Iran ya bada labari a jiya laraba cewa a cikin wadanda aka kashe a hare-haren har da wasu mata ukku da dan jariri. Kuma ana kyautata cewa yawan wadanda su ka mutu zai karu.

Kungiyar Jundallah ta ‘yan Sunni masu tawaye ta dauki alhakin kai munanan hare-haren na lardin Sistan-Baluchistan,a kusa da kan iyakar Iran da Pakistan. ‘Yan kungiyar Jundallah sun ce hare-haren na ramuwar gayya ne saboda kisan da aka yiwa shugaban su, Abdulmalek Rigi a cikin watan yunin da ya gabata.

Bama-baman sun tashi ne daf da wani Masallacin da masu ibada su ka tattaru a ciki albarkacin Ashura, daya daga cikin muhimman tsarkakkun ranaku ga Musulmi ‘Yan Shi’a.

Rahotannin da su ka fito daga kasar Iran sun nuna cewa daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ya ragargaza kan shi a kofar Masallacin sannan kuma wani ya tada wasu bama-baman a tsakiyar taron masu ibada. Haka kuma an ce ‘yan sanda sun gane dayan su, har ma su ka harbe shi su ka ji mi shi ciwo kafin ya farfasa na shi bama-baman.

Mataimakin ministan harakokin cikin gidan kasar Iran, Ali Abdolahi, ya ce jami’an tsaro na da shaidar da ta nuna cewa da goyon bayan Amurka da na wasu hukumomin leken asirin wasu kasashen yankin aka kai hare-haren.

Gwamnatin Amurka ta musanta wannan ikirari sannan kuma shugaba Barack Obama ya yi tur da Allah waddai da hare-haren da ya bayyana da cewa abun kyama, kuma aikin matsorata.