Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Shiga Jerin kasashen Afirka Masu Arzikin Mai.


A wan hoto shugaban Ghana John Atta Mills ne biyu, yana bude kan famfon mai a rijiyar tonon mai ta Nkwame Nkrumah dake takoradi a yinin yau Laraba.
A wan hoto shugaban Ghana John Atta Mills ne biyu, yana bude kan famfon mai a rijiyar tonon mai ta Nkwame Nkrumah dake takoradi a yinin yau Laraba.

Laraban nan ne Shugaban kasar Parfessa Atta Mills ya yi bikin kaddamar shirin haka da daukar mai daga kasar, da aka yi daga gabar teku da ake kira na Guinea.

Ghana ta shiga sahun kasashen Afirka masu arziki mai. Shugaban kasar Parfessa Atta Mills ne ya yi bikin bude famfunan mai na gwaji,da aka nuna kai tsaye ta kafofin yada labaran kasar daga wani jirgin ruwan dake matsayar Depo, a gabar Guinea.

Shugaban yace mai zai kasance alheri ga kasar Ghana ba fitina ba. A kasashe makwabta kamar Najeriya, mai ya janyo cin hanci da rashawa,da rigingimun cikin gida, yayinda jama’a kuma basu amfana ba.

Ghana tana daya daga cikin kasashen Afirka mafiya lumana,duk da haka masu fashin baki suna kashedin gwamnati bata zartas da doka da zate kare kudaden shiga da aka samu daga mai.

Babban kamfanin dake hakomai a kasar,mai suna Tullow Oil,daga Britaniya,yace da farko zai fara da hako ganga dubu 55 ako wace rana. Ana sa ran yawan mai da ake hakowa ya karu zuwa ganga dubu 120,000 ko wace rana zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG