Manoman Tumatir Sun Ce Kwastam Na Ja Musu Asarar Miliyoyin Naira

Manoman Tumatir a Najeria

Manoma Tumatir a Najeriya sun ce hukumar kwastam da takwararta ta NAFDAC mai kula da harkokin ingancin abinci da magunguna ta kasa, sun sa sun yi asarar kimanin Naira Miliyan dubu goma a kakar noman tumatir ta bana.

A yayin wani taro da manema labarai a Kano, shugabannin kungiyar manoman Tumatir din sun bayyana damuwa kan yadda hukumomin biyu ke zagon kasa ga sha’anin bunkasa noman tumatir a Najeriya.

Alhaji Sani Danladi Yadakwari, shine sakataren kungiyar na kasa, ya ce tumatirin da ake shigowa da shi daga kasashen ketare ya sa manoma asara. Ya kuma ce duk da dokar da majalisar zartarwar Najeriya ta yi akan shigo da Tumatir hukumomin kwastam da NAFDAC suna kawar da kai akan abubuwan da ke faruwa.

Alhaji sani ya kuma ce har yanzu ba su sami wani bayani daga gwamnati ba akan korafin da suka yi.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Manoman Tumatir a Najeriya Sun Koka Akan Asarar da Suka Yi Bana - 3'38"