Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar da Shirin ba Wasu Manoma Tallafi A jihar Adamawa


A karshen makon jiya ne hukumar UNDP tare da hadin gwiwa da gwamnatin kasar Japan suka kaddamar da shirin bada kayan noma kyauta ga mazauna kauyen Loko, na karamar hukumar Song a jihar Adamawa.

Wannan tsarin na daga cikin kokarin da hukumar UNDP ke yi na farfado da al’ummomin da tarzomar Boko Haram ta shafa a jihohin Yobe, Borno da Adamawa.

A karkashin sabon tsarin wanda gwamnatin Japan zata bada gudunmuwar dala miliyan biyu da rabi, an kiyasata manoma 2,200 da masu kananan sana’o’i 500 ne zasu ci gajiyar sa a kauyen.

Karkashin tsarin tallafin noman na hukumar ta UNDP, anyi tanadin raba kayayyakin noma ga magidanta 9000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kayayyakin sun hada da irin shuka, da magungunan feshin Kwari da takin zamani da sauran kayayyakin noma. Sai dai daraktan hukumar UNDP a Najeriya, Betty Wabunoha ta ce za’a bada kulawa ta musamman ga magidanta mata da suka rasa mazajensu sanadiyyar tarzomar Boko Haram.

Sai dai kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida, musamman wadanda ke sanya ido akan makomar iyalan da rikicin Boko Haram ya ritsa da su, sun ce akwai bukatar hukumomin ketare da suka bullo da wannan shirin su dauki matakai domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Kungiyar CAJA na cikin wadannan kungiyoyin kuma Comrade Kabiru Sa’idu Dakata daraktan kungiyar,ya fadi cewa yawan lokaci wadanda ake bada tallafin dominsu ba sa samu.

Shi kuwa Comrade Nura Iro, Ma’aji na kungiyar CISLAC ya ce, akwai bukatar a dinga bibiyar yadda masu cin gajiyar shirin ke tafiyar da harkokinsu don tabbatar da an aiwatar da shirin yadda ya dace.

Baya ga shirin tallafin noma, hukumar ta UNDP zata sake gina kauyuka 5 da kungiyar Boko Haram ta rusa kana an kiyasta magidanta 850 zasu sami guraben ayyuka a karkashin shirin.

Saurari rahoton Ibrahim Abdul'aziz

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG