Sashen Hausa ya zagaya cikin wata anuguwa a Birnin Abuja babban Birnin Nigeria domin jin ra’ayin mutane akan labarum da suke ji ko suke karantawa daga kafofin labaru musamman rediyo.
An anguwar Garki Alhassan Idris wanda aka fara tambaya ko ya san inda shugaba Buhari yake sai ya ce ya ji a rediyo ya tafi London domin a sake duba lafiyarsa saboda zaben dake tafe. Ya amince ya je hutu ne amma ya ce yana bukatar a dan dubashi.
Alhassan Idris ya manta suna shugaban hukumar DSS da ya rasa mukaminsa kwanaki biyu da suka gabata. Ya ji mataimakin shugaban kasa ya saukar dashi kuma tuni ya maye gurbinsa da wani.
Alhassan ya san cikakken sunanyen ministan shari’a da shugaban jam’iyyar APC. Akan dalilin da ya sa aka kwape shugaban DSS sai ya ce Shugaba Buhari ya daukoshi ya yi aiki amma sai ya kauce hanya yana kasuwanci da mukaminsa. Baicin hakan, a bangaren shugaban kasa abun da ya dace ne shi ya sa suka yi waje dashi.
Shi ko Suleiman Umar bai san sunan ministar kudin Nigeria ba saboda ya watsar da sauraron labarai. Ba ya sauraron duk labarin da ya shafi kudi domin, a cewarsa abubuwa basa tafiya kamar yadda ya taso ya gani. Dalili ke nan da ya dena domin kada ya jawowa kansa hawan jini. A lokacin Sanusi Lamido ya kan saurari labaru.
Abubakar Ibrahim bai san cikakken sunan ministan Abuja ba. Ya ce idan an san sunan mutum yana yiwa mutane adalci ne. Bai san sunan shugaban ma’aikata ba dake fadar shugaba Buhari domin shi ma ba ya yiwa mutane adalci.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya domin karin bayani
Facebook Forum