Sai dai masu sharhi akan harkokin noman alkamar da sarrafata a kamfanoni sun ce gwamnati na da damar daukar matakan da zasu kubutar da manoman daga tafka asara.
Kamar sauran kasahen dunuya, rikicin da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine ya yi mummunan tasiri ga cinikayya da sarrafa alkama a Najeriya, la'akari da muhimmancin kasahen biyu ta fuskar nomawa da samar da alkama ga duniya.
A duk shekara, Najeriya na sayan adadi mai yawa na alkama daga ketare.
Tarzomar dake wakana a Rasha da Ukraine kusan shekaru biyu da suka gabata ta haifar da karancin alkamar da kamfanonin fulawa na Najeriya ke sarrafawa su mayar da ita nau'ukan abinci daban daban.
Hakance ta sanya hukumomi suka karfafa gwiwar manoman kasar su rungumi aikin noman alkama da nufin cike wani adadi na gibin da aka samu.
Tuni dai manoman suka amsa wannan kira na mahukunta, musamman a jihohin Kano da Jigawa. Sai dai manoman na korafi kan yadda suka ce kamfanonin Fulawa sun yi biris da su dangane da batun fitar da farashin alkamar a bana.
Alhaji Ali Yunusa Yandutse shine shugaban kungiyar manoma da cinikayyar amfanin gona a jihar Jigawa ya bayyana damuwa kan wahalhalun da ‘yayan kungiyar suke fuskanta a noman bana, amma gashi kamfanoni sun yi biris da su.
‘’Ya ce manoman sun sha wahala, sun yi aikin nan ga wahalar man fetir ga wahalar canjin kudi da ya rintsa da su a kwanakin baya amma ba su fasa ba, kuma amfani ya yi kyau sai dai kamfanoni Fulawa sun yi biris da batun farashi.”
Sai da i Alhaji Babangida Lamido, wani mai kula da lamura a fannin hada hadar kayayyakin abinci masu nasaba da Fulawa ya ce kalubalen da manoman alkamar ke fuskanta ba zai rasa nasaba da sarkakiya irin ta diplomasiyya tsakanin kasa da kasa ba.
“Gwamnatin tarayya ce keda alhakin tafiyar da harkar alkama, muna karbo kaya daga Amurka muna basu mai alkama tana ciki. Ko a lokacin shugaba Babangida an yi wannan yunkuri na noman alkama a cikin gida, amma lamarin ya ci tura”
Bincike ya nuna cewa, kusan kowane gida a Najeriya na amfani da daya ko biyu na nau’in cimakar da aka samar daga alkama a kowace rana.
Ga rahoton Mahmud Kwari cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5