Gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da sayar wa manoma takin zamani ton dubu 15 akan farashin gwamnati na Nera dubu biyar da dari biyar kowane buhun takin.
Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello shi ya kaddamar da sayar da takin inda ya gargadi jami’ansa da su guji karkata sayar da takin zuwa kasuwar bayan fage.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnati ta kebe filin noma kadada sama da dubu biyar a sassa daban daban a jihar a karkashin shirin bunkasa aikin noma domin karawa matasa karfin gwuiwa akan aikin noman.
Kwamishanan kula da harkokin noma na jihar Alhaji Haruna Dukku yace a bana sun yi tsarin da zai hana yin cuwa cuwa wajen sayar da takin.
A cewarsa kowace tirela za’a rakata har zuwa shagon da za’a jibge takin, kuma jami’an tsaro zasu kula da takin har a kammala sayar dashi.
Alhaji Shehu Galadima shugaban hadakar kungiyoyin manoma a jihar yace sun gamsu da tsarin da aka bayyana masu amma sai sun gani a kasa saboda wani sailin wanda aka ba amanar abu shi ne zai ci amana. Ya ce su manoma zasu dauki nasu matakin. Zasu sa ido a koina su tabbatar an aiwatar da Gaskiya. Ya yi kira ga gwamnati data dauki matakin da ba zai cutar da manoma ba.
Bugu da kari gwamnatin jihar ta ce ta sayo tiraktoci dari da hamsin domin anfanin manoman akan kudi Nera miliyan dubu biyu da miliyan dari biyu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5