Ma’aikatan gwamnatin jihar Neja sun gudanar da bikin ranar ma’aikata a cikin wani yanayi na rashin walwala sanadiyar rashin samun kudadensu na alawus alawus.
Bala Moni Abdulkarim na cikin wadanda suka fito macin a ranar ta ‘yan kwadago yana cewa albashi ya yi kadan, kudin zuwa hutu an daina biyansu, kudin tafiya yin aiki waje ma babu sai dai ma’aikaci ya yi anfani da nashi kudin. Ya roki gwamnati ta taimaka ta duba yiwuwar kara albashin ma’aikata.
Wani mutum mai suna Bala yace, albashin wanda yak e mataki na sha biyu, Naira 46,000 ne kacal ya ke karba a wata. Yace shi kansa da yake kan mataki na 14, Naira 61,000 yake samu wata.
Sai dai gwamnatin jihar Neja ta ce tana sane da matsalolin ma’aikatan. Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce suna kokarin shawo kan lamarin. Yace sun gabatar da bukatu wajen goma kuma wasu hakkinsu ne sai dai yanayin kudi ba zai bari gwamnati ta iya aiwatar dasu yanzu ba. Ya yi alkawarin duba batun kudin hutu ya ga abun da gwamnati zata iya yi. Haka ma batun kara girma da aka dade ba’a yi ba za’a duba.
Ma’aikatan sun gamsu da bayanan gwamnan kana wasu sun nuna jin dadin halartar bikin da gwamnan ya yi abun da bai faru ba cikin shekaru uku da suka gabata.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da kain bayani
Facebook Forum