Manoman Jahar Naija Na Kukan Rashin Takin Zamani

Wata gona a yankin arewacin Najeriya

Rashin isasshen takin zamani na yiwa manoma cikas a Najeriya, musamman ma a yankin arewacin kasar
A yayin da damana ta kankama haikan a yankin arewacin Najeriya, manoman yankin na ci gaba da kokawa game da rashin samun takin zamanin da za su yi amfani da shi a gonakin su.

Takin zamani dai na daga cikin muhimman abubuwan da manoman ke bukata wajen noma wadataccen abincin da al’ummar kasa za ta yi amfani da shi.

A kusan kowace shekara dai manoman, musamman ma na yankin arewacin Najeriya na yin korafin rashin samun takin zamanin cikin lokaci, al’amarin da ke matukar kawo mu su cikas wajen samun kyakkyawar yabanya. Wakilin Sashen Hausa a jahar Naija Mustapha Nasiru Batsari ya tattauna da wasu manoman jahar wadanda su ka gabatar da koken su da korafin s kamar haka:

Your browser doesn’t support HTML5

Manoman jahar Naija sun koka da rashin taki - 2:04