Jami’ai sunce a gundumomin Gao da Asongo kadai cutar ta kama mutane 147, har ta kashe 12 daga cikinsu daga lokacinda ta soma bulla a watan Yulin nan da ya gabata. Yanayin ruwan saman da aka shiga yana kara wanzuwar cutar.
Babbar Jami’ar yaki da wannan cutar ta Kungiyar IRC (International Rescue Committee), Tasha Gil ta shawarci al’ummar kasar ta Mali da cewa da zarab sun ga alamar wannan cutar ta kama wani, kada a bata lokaci, a hanzarta garzayawa zuwa wajen likitoci.
Tun dai watan Aprilun wannan shekarar, ‘yan al-Qaida suke rike da sashen arewancin kasar ta Mali. Ms. Gil tace yanzu ne aka sake komawa ga wani kyamfe da ake gudanarwa a gidajen rediyo bayanda ‘yan kishin Islama din suka bayyana rashin amincewa da wasu kade-kade da wake-waken da ake anfani da su a cikin sanarwowin da ake watsawa.
Ko bayan Mali, an bada rahoton barkewar cutar kolera din a kasashen Junhuriyar Nijer, Guinea da Saliyo.