Manoma Da Masana’antu Na Ci Gaba Da Bayyana Damuwa Akan Hauhawar Farashin Man Dizal

Manoma

Yan Najeriya, musamman manoma da mamallaka kamfanoni da masana’antu na ci gaba da bayyana damuwa akan hauhawar farashin man dizal, da ke haifar da tsadar safarar kayayyaki zuwa bangarori daban daban na kasar.

Kusan dukan motocin dakon kaya dake zirga-zirga a kasar na amfani ne da sinadarin man dizal, baya ga injinan da ake amfani da su wajen sarrafa kayayyaki a masana’antu da kuma wadanda ke bada hasken lantarki a ma’aikatu, gidaje da kuma hukumomin gwamnati, duka na amfani ne da sinadarin na man dizal.

Yanzu haka dai ana sayar da lita guda ta man dizal akan naira 750 zuwa 800, sabanin naira 350 zuwa 400 da aka saya ‘yan watannin baya can.

Alhaji sani Hussaini shugaban kungiyar masu masana’antu ta Najeriya mai kula da shiyyar Kano da Jigawa ya ce tsabar tsaddar dizel ya kai ga yawancin masana'antu ba ma iya kunna inji idan aka dauke wuta.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mamallaka kamfanonin samar da bakin mai da dangogin sa a Najeriya ke maraba da ragin kashi 5% na karin da gwamnati tayi akan kudin fiton sinadaran da suke amfani dasu, amma sunce tsadar da man dizal ke yi zata hana tasirin da ya kamata ga wannan rangwame.

A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Mustafa Ado Muhammad shugaban kungiyar na kasa, ya tabbatar da cewa za su rage amma sai sun yi dogon nazari.

Su-ma masu noman alkama na kokawa akan wannan tsada ta man dizal, kamar yadda Dr Salim Sale Muhammad shugaban kungiyar manoman alkama ta Najeriya ya shaidawa Muryar Amurka.

Hakan dai na kara fito da tasirin wannan sinadarin man na dizal ga rayuwar ‘yan kasa da kuma bukatar dake akwai ga mahukunta su gaggauta daukar matakan da suka kamata domin magance wannan matsala.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Manoma Da Masana’antu Na Ci Gaba Da Bayyana Damuwa Akan Hauhawar Farashin Man Dizal:3:00"