Shugaban kungiyar manoma shinkafa ta kasa reshen jihar Adamawa Alhaji Abdullahi Maikano Tafida, ya yi zargin cusa siyasa a harkar noma lokacin da yake maida martini ga sanarwar da kwamishinan ma’aikatar noma na jiha Alhaji Ahmed Waziri ya bayar a madadin kwamitin da ya hada bankin tarayya, bankin manoma, kanfanin inshorar nomad a ma’aikatarsa wanda yake shugabanci cewa za a samarwa Kananan manoma dubu ashirin datakwas rancen naira dubu dari da sitting a kowane manomi na noma kadada daya domin bunkasa ayukan noma.
Sanarwar ta gamu da kakkausar suka lokacin da ma’aikatar ta ce ta rage yawan kadada da manoman suka nema daga daya zuwa biyar kamar yadda shirin ya tanada zuwa kadada daya kacal kana kuma ta zabtare kudin rance da aka aiyana naira dubu dari biyu da ashirin ga kawani kadada. Tsarin da wani karamin manomi Mal. Sadiq Jimeta ya bayyana da yaudara.
Saurari rahotan Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5