Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Jihar Oyo Ta Kama Wasu Masu Aikata Manyan Laifuka


IBRAHIM K. IDRIS babban sifeton 'yansandan Najeriya
IBRAHIM K. IDRIS babban sifeton 'yansandan Najeriya

Wadanda rundunar ta kama sun hada da masu kira kudin jabu da fashi da makami da satar mutane, da satar motoci da masu sayen kayan sata da dai sauransu.

Kwamishanan 'yansandan jihar shi ya gabatar da masu laifukan da suka kama su wajen arba'in da bakwai a gaban manema labarai.

Rundunar 'yansandan ta roki jama'ar jihar su dinga tsegunta masu da labarin muggan mutane da mabuyarsu tare da masu taimaka masu.

Wasu da suke sayan kayan sata sun zanta da Muryar Amurka. Wani Femi Fakoya dan shekaru 66 da haihuwa yace an kamashi da sarafa kudin jabu. Yace ya kan yi anfani da naurar daukan hoto mai launi ya dauki hotunan kudade.

Shi ma Abdullahi Adamu yana sayen kayan sata ne. Ya je Ogbomosho sayan babur tun daga jihar Neja. Ya saba sayen babura daga wurin mutumin.

Abubuwan da aka gano daga hannun barayin sun hada da motoci da naurar sa ruwan sha sanyi da babura da naurori masu kwakwalwa har da ma wayoyin salula.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG