An bayyana hakan ne a karshen taron shugabanin kungiyar yan fensho na jihohin Arewa maso Gabas a Bauchi. Mataimakin shugaban ‘yan Fansho na wannan shiyya Mohammad Inuwa Ahmed Dan, yace halin da ‘yan Fanshon ke fuskanta a Najeriya shine dalilin taron da Bauchi, ya kuma nuna cewa wasu jihohi kan yi iyaka kokarinsu na ganin sun biya kudaden da ake binsu amma wasu basa kokari ko kadan.
Taron dai na jawo hankulan gwamnatocin da cewa su tuna cewar ‘yan Fanshon nan mutane ne da suka bautawa ‘kasa, kuma suyi la’akari da yawan da ‘yan fensho domin zasu iya nuna banbanci a lokacin zabe.
Shugaban kungiyar masu karbar Fansho a jihar Taraba Kwamarad Hassan Abubakar, yace matsalolin kusa ‘daya ne a dukkannin jihohin sai dai a Tarabar akwai dan banbanci.
Saurari cikakken rahotan.