Manchester City Za Ta kara Da Copenhagen

Champions League

Za a fara wasannin farko a watan Fabrairu sannan a buga zagaye na biyu a Maris din 2024.

Manchester City, wadda a bara ta yi nasarar lashe kofin zakarun nahiyar turai, za ta kara da FC Copenhagen a zagaye na biyu na gasar a bana, bayan an shirya jadawalin zagaye na biyu yau, Litinin 18 ga watan Disamba.

A sauran wasanni da za a kara a zagayen na biyu, Arsenal wadda ta ja rukuni na biyu za ta fafata da FC Porto da ta kare na biyu a rukuninta da Barcelona ta jagoranta.

Ita Barcelona za ta kara da kulob din Victor Osimhen wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar CAF, Napoli. Bayern Munich na kasar Jamus za ta yi gurmuzu da Lazio, sai kuma RB Leipzig ta kasar Jamus wadda za ta karbi bakoncin Real Madrid ta kasar Spaniya a filin wasanta na Red Bull Arena.

Haka kuma Atletico Madrid za ta marabci Inter Milan a filin Metropolitano.

Za a fara wasannin farko a watan Fabrairu sannan a buga zagaye na biyu a Maris din 2024.

Za a buga wasan karshe na gasar zakarun turai ta bana a filin wasa na Wembley da ke Landan a ranar 1 ga watan Yuni.

Ga cikakkiyar jadawalin Gasar Zakarun Nahiyan Turai zagaye na biyu

  • Porto da Arsenal
  • Napoli da Barcelona
  • PSG da Real Sociedad
  • Inter Milan da Atletico Madrid
  • PSV Eindhoven da Borussia Dortmund
  • Lazio da Bayern Munich
  • Copenhagen da Manchester City
  • RB Leipzig da Real Madrid