Manchester City Ta Fara Kare Kofin Premier League Da Ta Lashe

'Yan Wasan Manchester City

A ranar Juma’a gasar ta Premier ta bana za ta kankama, inda City za ta kai wa Burnley ziyara a gidanta a wasan farko.

Kungiyar Manchester City da ta lashe kofin gasar Premier League a bara za ta fara kare kofinta.

A ranar Juma’a gasar ta Premier ta bana za ta kankama, inda City za ta kai wa Burnley ziyara a gidanta a wasan farko.

Vincent Kompany, wanda tsohon dan wasan City ne yake horar da Burnley.

Shararsa a kungiyar, har ta kai ga an yi mutum-mutuminsa a kofar filin wasan na City a Manchester.

Ita dai City ta wataya a kakar wasa ta bara inda ta lashe kofin Premier League, FA Cup da kuma kofin gasar zakarun turai na Champions League.

Ana fatan City za ta gabatar da Josko Gvardiol a matsayin sabon dan wasanta wanda dan asalin kasar Croatia ne.

Gvardiol ya yi kaura ne daga Leipzig a makon da ya gabata.