Yayin da aka shiga mako na 11 a gasar Premier League na kakar wasannin 2021-2022, Manchester City ta doke Manchester United da ci 2-0 a ranar Asabar.
A kwallon farko Manchester United ce ta ci gida ta hannun dan wasanta Eric Bailly.
Daga baya kuma dan wasan City Bernardo Silva ya zura kwallo ta biyu.
Wannan karawa ta kara fito da matsalar da masu fashin baki ke cewa United na fuskanta ta rashin kwararan masu tsaron gida.
Da ba don mai tsaron ragar United David de Gea ya doke wasu kwallaye ba, da yaran na Pep Guardiola sun zura wasu karin kwallaye.
Wannan kaye shi ne na hudu da United ta sha a manyan wasanni shida da ta buga, shi ne kuma na biyu a kayen da ta sha gida.
Sakamakon wannan wasa ya ba City damar matsawa zuwa matsayi na biyu a teburin gasar ta Premier.
Har ila yau hakan ya ba City damar rage ratar da Chelsea ta ba ta.
Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?
Your browser doesn’t support HTML5