Duk da cewa an kwana biyu bayan kayen da Manchester United ta sha a hannun Liverpool a karshen makon da ya gabata, har yanzu kurar da wannan wasa ya tayar ba ta kwanta ba.
Wasan ya sa masu sharhi na ta fashin baki kan batutuwan da suka shafi makomar kocin United Ole Gunner Solskjaer, bayan da Liverpool ta doke Manchester United da ci 5-0 – a Old Trafford.
Yayin da wasu ke haska fitilarsu akan wasu fannonin wannan wasan, wasu kuwa sun mayar da hankalinsu ne kan Paul Pogba wanda ya shiga wasan bayan da aka ajiye shi a benci.
Masu lura da al’amura sun ce hakan bai yi wa Pogba dadi ba duk da cewa an sako shi bayan rabin hutun lokaci inda ya canji Mason Greenwood.
Sai dai minti 16 kawai Pogba ya buga a wasan aka maka masa jan katin sallama, bayan da ya yi wa dan wasan Liverpool Naby Keita shigar keta lamarin da ya sa aka fita da Keita a gadon marasa lafiya a filin.
Wasu na ganin halayyar da Pogba ya nuna ta taka Keita, alama ce ta fushin ajiye shi da Solskjaer ya yi a benci.
“Ya yi matukar fushi ne, dalilin kenan da ya sa har ya kai ga an ba shi jan kati, ina kuma ganin idan Manchester United ta ci gaba a haka, ina ganin zai tafi.” Tsohon dan wasan Faransa Frank Leboeuf ya fadawa ESPN.
Shi dai Pogba bai sabunta kwantraginsa da United ba wanda zai kare a karshen wannan kakar wasanni.
Wasu rahotanni sun ce akwai alamu da ke nuna cewa dan wasan wanda dan asalin kasar Faransa ne ya koma kungiyarsa ta Juventus da ke Italiya wacce ya takawa leda a tsakanin 2012-2016.
Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?