Shugaban mulkin sojan kasar Mali Kanal Assimi Goita ya fada a ranar Lahadi cewa, nan ba da jimawa ba kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar za su kaddamar da sabbin fasfo, a daidai lokacin da kasashen da ke karkashin mulkin soja ke kokarin tabbatar da kawancensu bayan ballewarsu daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS.
Kasashen uku na yankin Sahel, wadanda ke karkashin mulki soji, biyo bayan juyin mulki da aka fara yi tun 2020, sun hade ne a watan Satumbar bara a karkashin kawance kasashen Sahel (AES), bayan da suka yanke alaka da tsohuwar wacce ta yi musu mulkin mallaka kasar Faransa tare da karkata zuwa kasar ga kasar Rasha.
Sun fada a cikin watan Janairun da ya wuce cewa, sun fice daga kungiyar kasashen raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, kungiyar da suka zarga da cewa Faransa na amfani da ita.
A cikin watan Yuli, kawayen sun kulla alakarsu tare da kafa kungiyar hadin kan yankin Sahel, wadda za ta kasance karkashin jagorancin kasar Mali a shekarar farko da kungiyar ta kunshi kimanin mutum miliyan 72.
Goita ya fada yayin wani jawabi da aka watsa ta talabijin da yammacin ranar Lahadi cewa “A cikin kwanakin masu zuwa, za’a sanya sabon fasfo na AES da nufin daidaita takardun balaguro a yankinmu.”
Ya ce “Za mu yi aiki don samar da abin da ake bukata don karfafa cudanya a yankunanmu ta hanyar sufuri, hanyoyin sadarwa da fasahar sadarwa.”
Sanarwar ta zo ne kwana guda gabanin bikin cikar kasashen uku na cika shekara guda da kafa kungiyar.
Kasashen wadanda makwabtan juna ne duka suna fama da rikicin masu ikirarin jihadi da ya barke a arewacin Mali a shekarar 2012 ya kuma bazu zuwa Nijar da Burkina Faso a shekarar 2015.
An yi kiyasin cewa rikicin ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu a fadin yankin.
AFP