MALAYSIA: Frayim Ministan Kasar Ya Musanta Zargin Karban Na Goro

Najib Razak Firayim Ministan Malaysia

Frayim-ministan Malaysia, Najib Razak yayi watsi da rahotan nan da ake watsawa, cewa ya karbi toshiyarbaki ta kudi sama da dalar Amurka miliyan 700 daga wani kamfanin zuba jari na gwamnati.

Jaridar Wall Street Journal da wata mujallar kasar ta Malaysia ne suka bada labarin, bisa bayanan da suka daga rahoton binciken wani kamfani mai suna “1MDB” da aka bayar.

Rahotan yace an aika da kudade masu dimbin yawa har sau biyu zuwa asusun bankin Mr. Najib, inda, da farko aka zuba Dala miliyan 620 sannan kuma aka kara miliyan 61 a lokacin kamfen din zaben da akayi na shekara ta 2013.

Shi dai wannan kampanin, wanda Mr. Najib ke jagoranta, ana zarginsa da laifukkan cin hanci da rashawa kumayanzu haka ana binsa bashin sama da Dala miliyan dubu 11. haka kuma ma’aikatun gwamnati da dama suna gudanarda bincike iri-iri akansa, ciki harda wanda Babban Bankin kasar ke gudanarwa.