Wani farfesa na jami’ar A & M dake Jihar Texas anan Amurka yace, daukacin ‘yan ajinsa dayake koyarwa na kwas din dabarun mulki da tattali sun yi rashin gaskiya da tursasawa, Kuma zasu fuskanci hukunci, sai hukumar jami’ar tace wannan ba zata sabu ba. kamar yadda wani kafar sadarwar jami’ar ya bayyana.
Farfesa Irwin Horwirz ya aika da sako ne ta yanar gizo a cikin satin daya shige, yana mai cewa yana da magana da daukacin dalibansa su 30 musammam akan jarabawar su, wanda kusan dukkan su ba wanda yaci wannan jarabawar, kuma yana da labarin cewa sun ce yana musu rashin gaskiya wajen jarabawa.
Ga ma abinda yake cewa a cikin sakon yanar gizon da ya aika, a gani na ba wanda ya cancanci ace yaci wannan jarabawar har ya zamo ya samu digirin wannan jami’ar idan aka yi la’akari da ‘dabi’ar ku.
Sai dai ba a samu wani daga cikin jami’ar ba domin jin ra’ayin sa game da wannan batu.
Amma hukumar jami’ar ta shaidawa gidan talabijin din KRPC cewa tana binciken wannan batu na farfesa Horwirz, batun cewa ba zasu ci jarabawar sa ma bata taso ba sai dai idan da gaske ne dalibi baici jarabawar tasa ba, wannan ne ma yasa yanzu aka cimma matsaya cewa shugaban sashen ne zai cigaba da koyar da daliban har sai an kai karshen zangon karatu.