Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2015 Ya Wuce Ya Bar Baya Da Kura Ga Matasa


Masu yima kasa bauta a lokacin zaben 2015
Masu yima kasa bauta a lokacin zaben 2015

Kadan daga cikin wasu dalilai da ke sa ana yadda akeso da kuri’un jama’a kenan a lokacin zabe. Wasu matasa masu yima kasa hidima da kuma sukayi aikin zabe da aka gudanar na shugaban kasa da ma na gwamnoni a zaben daya gabata, basu samu an basu hakkokinsu ba har yau kimanin wata daya kenan da sukayi wannan aikin.

Wasu daga cikin dalilan da suke haifar da aiwatar da magudi ke nan a lokacin zabe, kasancewar su malaman zabe basu da wadata, wadda ta haka ne ‘yan siyasa kanyi amfani da wannan dammar don sayesu, da kuma yin duk wasu ayyuka da suka sabama ka’idojin zabe.

Masana naganin idan har ba’a magance wannan matsalar na bama kowa hakkinshi ba a lokacin daya dace ba, to lallai babu yadda za’ayi a kaucema wannan matsalar ta aikata abubuwan assha a lokaci da baya zabe, don ta haka ne kawai irin wadannan ma’aikatan bazasu sa kansu cikin wasu hali na neman abun duniya ba tako yaya.

A korafi da wadannan matasan masu yima kasa hidima suka gabatar sun nuna cewar tun bayan wannan aikin, anbukace su dasu bada lambar assusun ajiyansu na banki wanda suka bada ya kai har sau fiyar amma haryau shuru kakeji, kuma sun samu labarin an biya wasu amma nasu har yanzu babu wata kwakwarar magana. A wannan ne yasa suka kawo kukansu don a duba kuma a share mushu hawayensu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG