Yanzu haka ana ci gaba da cece-kuce tare da bayyana mabambantan ra'ayoyi kan samamen da wasu da ake zargin jami'an tsaro ne suka kai a gidan alkaliyar kotun kolin Najeriya, mai shari’a Mary Odili.
Wasu da dama suna ci gaba da zargin Ministan shari’a Abubakar Malami da hannu kan wannan samamen, lamarin da ya sa shi kuma yake kara nisanta kansa daga samamen.
Na baya-bayan nan dai shi ne lokacin da yake amsa tambayoyi kan gaskiyar lamarin a cikin shirin Siyasa A Yau na gidan talabijin na Channles inda ya musanta duk wata alaka tsakanin ofishinsa da madugun wadanda ake zargi da hannu a kutsen da aka kai gidan mai shari’a Mary Odili.
Malami ya nanata cewa shi da ofishinsa ba su da alaka a hukumance ko ta bayan fagge da madugun kai samamen wato Lawrence Ajodo, da sauran mutane 13 da aka kama bisa zargin yin kutse gida Mary Odili.
A cikin makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta sami nasarar kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kutsen da aka kai gidan alkaliyar ta kotun koli, mai shari’a Mary Odili, da ke birnin Abuja ciki har da madugun su, Lawrence Ajodo, wanda ya ce ya taba yin aiki da antoni janar na tarayyar Najeriya Abubakar Malami.
Ministan ya kara da cewa bai taba yin aiki da Lawrence Ajodo ba ya na mai cewa idan akwai wani aiki da ya taba ba wa wanda ake zargin, ya kawo shaidar hakan.
A cewar Malami, bai taba ko sanya Lawrence Ajodo a ido ba kuma ya yi imani cewa banda aikata laifin kutse akwai alamar tambaya a cikin lamarin da ya kamata rundunar yan sanda da ke da alhakin binciken lamarin ta gudanar da bincike mai zurfi don gano gaskiyar lamarin.
Haka kuma, Malami yace wanda ake zargin ba ya cikin tsarin biyan albashin ma’aikatar shari’a ta tarayyar kasar, kuma idan da ma’aikacin gwamnati ne ba zai gudanar da ayyukan da suka saba wa tsarin ma’aikatar ba.
"Ana gudanar da aikin gwamnati ta hanyoyin da suka dace, don haka, ba zai yiwu wani sashen ofishin antoni janar na aikin kashin kansa ba ko kuma aiki ba bisa ka'idar doka ba" in ji Malami.
Idan ana iya tunawa, wasu gungun mutane sun yi kutse a gidan mai shari’a Odili a ranar 29 ga watan Oktoba, saidai har yanzu ana ci gaba da yin tambayoyi akan wanda ya aika a yi kutsen daga farko.
Da farkon kai kutsen dai an yi zargin cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ce ta kai samamen domin gudanar da bincike a kan mijin Mary Odili wato tsohon gwamnan jihar Rivers, Peter Odili, sai dai kuma hukumar ta bakin shugabanta Abdulrasheed Bawa, ta nisanta kanta da kai samamen, tana mai cewa babu wani jami’inta da ya ke wurin.
Baya ga haka gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi zargin cewa akwai yiyuwar an kai samamen ne don halaka iyalin Peter Odili inda ya ba wa gwamnatin tarayyar Najeriya sa'o'i 48 da ta binciko tare da hukunta duk wanda ke da hannu a aikata laifin cikin gaggawa.
Tun farkon lamarin kuma ofishin ministan shari'a ya nisanta kansa da zargin ba da umarnin kai samamen inda mai ba ministan shawarma kan harkokin yada labarai, Jirbril Gwandu ya ce kalaman madugun wadanda ake zargi da kai kutsen wato Lawrence Ajodo, na alakanta laifin da ake zarginsa da shi da ofisin ministan shari’a ba su da tushe balle makama.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya dai ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa babu hannun ma’aikatar shari'a a samamen da aka kai gidan mai shari’a Mary Odili.