Malamai sun sasanta tsakaninsu da hukumomin jahar Maradi kan matsalar rashin biyan malaman kwantiragi a Jamhuriyar Nijar kudadensu.
A wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka, babban magatakardar kungiyar malaman, Malam Sadisu Muhammad, ya ce duk matsalolin da suke takadaddama a kansu gwamnati ta amince da su.
Malaman sun shiga yajin aiki ne tun bayan da suka fara korafin ba a biyasu wasu kudadensu na alawus ba.
“Abinda muke fata shi ne dama gwamnati ta kira bisa teburin shawara mu tattauna bisa yarjejeniyar da aka yi, saboda haka kowa ya koma bisa kan aikinsa.” In ji Malam Sadisu Muhammad.
Malam dai sun kwashe kusan shekaru uku suna gwagwarmayar neman hakkokinsu da suka shafi inganta ayyukansu.
Ga karin bayani a hirar wakilinmu Chou'aibu Mani da Malam Sadisu Muhammad, babban Magatakardan kungiyar Malamai:
Your browser doesn’t support HTML5