A yayin zanga-zangar, malaman sun zargi Kananan Hukumomin Abuja da yin wasarere da batun jin dadi da walwalarsu.
Malaman sun gudanar da zanga-zangar ne akan rashin biyansu bashin da suke bi na kudaden albashi dana karin girma da kuma na mafi karancin albashi tun daga shekarar 2019.
Malaman sun bukaci Ministan Abuja, Nyesom wike da Shugaban Kasa Bola Tinubu su sa baki a lamarin.
Haka kuma sun yi kira da a sake fasalta tsarin ilmin firamare a kasar, inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta kwace ragamar gudanar da makarantun daga hannun kananan hukumomi.
Malaman firamaren birnin Abuja sun shafe fiye da mako guda suna yajin aiki amma har yanzu sun ce babu wani takamaiman martani daga hukumomin da alamarin ya shafa.