Kamfanonin zasu kula da harkokin 'yan kwantiragin ne kama daga cancantar samun aiki zuwa saka hannu akann kwantiragi har zuwa ga biyan albashi.
Malam Munkaila Halidu babban sakataren kungiyar 'yan kwantiragi yace kamfanonin da ba sa iya biyan albashi su ne zasu biya malaman kwantiragi?
Yace babu yadda zasu iya biyan malaman makaranta su dubu sittin da biyu. Idan gwamnati ce zata basu kudi su biya, ita ma gwamnatin bata biyan 'yan kwantiragi kan lokaci.
Su malaman suna bin gwamnatin albashin watanni biu ko hudu.Yace basu yadda da matakin da gwamnati ta dauka ba.Saboda haka suka kira shugaban kasa Mahammadou Issoufou ya tsige ministan ilimi.
Amma ofishin ministan makarantun firamare ya bayyana cewa akwai rashin fahimtar sabon matakin, saboda haka batun cire ministan bai taso ba, inji Malam Ashana Hima daraktan kula da cigaban ma'aikata a ofishin ministan.
Yace ba wai 'yan kwangilan zasu fita daga hannun gwamnati ba amma duk sha'anin firamare an mayar hannun kamfanoni, kenan duk wani malami dan kwantiragi dake koyaswa a firamare kamfononin zasu kula da lamuransa.
Gwamnati zata dinga tura kudinsu zuwa kamfanonin domin a biya malaman makaranta 'yan kwantiragi.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5