A karon farko hukumar kwastan ta kira taron manema labarai domin mayarda martani akan cecekucen da ya taso tsakanin gwamnati da kungiyar 'yan kasuwa da na dillalan awon kaya, Bolore
'Yan kasuwan suna adawa da matakin sakarwa kamfanin Bolore kayansu kafin a kayyade harajin da zasu biya.
'Yan kasuwan suna ganin wannan matakin zai tabarbar da harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasar.
Kanar Sale Abdu jami'in kula da harkokin doka ahukumar kwastan din yace matakin zai bada damar sanin yawan kawayan da kowa ya shigo dasu. Idan ba'a yi hakan ba sai abun da dan kasuwa ya ga dama ya fadi. Yace idan an sauke kaya kafin a yi masu kudin kwastan 'yan kasuwa zasu ji ba dadi saboda rashin fadin gaskiya. Yace ta wannan hanyar gwamnati zata samu karin kudin shiga sosai.
Amma babban sakataren kungiyar 'yan kasuwan dake shigo da kaya daga ketare yace duk harajin da aka sa masu zai koma kan talakawa ne. Gwamnati ta yi nata ikon amma 'yan kasuwa ke da iko da kayansu saboda haka za'a yi tsadar rayuwa. Matakin ya sa wasu sun doshi rushe rajistan kasuwanci da Nijar. Wasu ma sun bar shigowa da kayansu kasar.
Ga karin bayani.