Gwamnatin Nijar ta gina asibitin ne da tallafin kudi daga China wanda ayyukan gine ginenshi ya lakume kudi sama da miliyan dubu arba'in na sefa, wato kwatankwacin nera miliyan dari biyu da goma sha takwas (Nera 218,000,000).
Asibitin yana matsayin asibitin kwararru kuma yana da girman kwantar da mutane dari biyar a wani matakin inganta lafiyar jama'a musamman mata da yara kanana.
Ana kyautata zaton hakan zai takaita fitar mutane zuwa neman jinya a kasashen waje.
Yayinda yake karban mabudan asibitin daga hannun jakadan kasar China, Shugaban Nijar ya bayyana cewa asibitin shi ne mafi girma a duk kasashen Afirka ta Yamma. Ya mika godiyarsu ga kasar China wadda ta taimaka da gina asibitin.
Ministan kiwon lafiya Alhaji Kallamu Tari yace an tanadi naurori irin zamani da kwararrun likitoci 'yan Nijar da China da Turkawa da Cuba domin kula da mara sa lafiya a katafaren asibitin.
Talakawan da suka halarci bikin sun nuna farin ciki da samun asibitin amma da fatan gwamnati zata ba masu karamin karfi cin moriyar asibitin. Suna fata idan sun zo neman magani ba za'a ce su kawo kudin da zai kaiga sai sun sayan da gidajensu ba kafin su iya biya.
Akan asibitin gwamnan Yamai Hamidu Garba yace a nadawa asibitin sunan Issoufou Mahamadou. Amma ministan kiwon lafiya Kallamu Tari ya jingine wannan bukatar domin kaucewa duk wani cecekuce.
Ga karin bayani.