A babban birnin tarayya Abuja, malaman makarantun firamare sun sa murna ta koma ciki ga iyaye dake fatan komawar 'ya 'yansu makarantu, bayan kawo karshen zaman gida na tsawon watanni bakwai da gwamnatin tarayyar kasar ta yi, don shawo kan annobar COVID-19.
Malaman sun yanke shawarar tura dalibansu zuwa gida saboda rashin aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30, da aka yi musu alkawari.
Karkashin inuwar kungiyar malaman Najeriya ‘NUT’ reshen birnin tarayya Abuja, sun yi korafi a kan yadda shugabannin kananan hukumomin Abuja, suka ki aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 tare da sauran hakokkinsu.
Wani malamin makarantar firamare ta gwamnati dake Asokoro, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce tun bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar, a kan aiwatar da mafi karancin albashi a watan Afrilun 2019 ba a aiwatar da umarnin ba kuma tun watan Disamba 2019 ba a biya su sauran hakokinsu ba.
Da wakiliyar Muryar Amurka ta ziyarci makarantar firamare ta Model dake kan titin Nelson Mandela a Asokoro, wurin da sashin karamar sakandare ya ke, wasu daliban firamare sun bayyana yadda suka ji da rashin makaranta.
A wani bangare kuwa takwarorin su na bangaren karamar sakandare suna cikin azuzuwa sakamakon yadda hukumomin birnin tarayyar Abuja suke biyan albashinsu yadda ya kamata.
Tun watan Satumba ne shugaban kungiyar ‘NUT’ reshen birnin taraiya, Stephen Knabayi, ya shaidawa malamai duk lokacin da gwamnati ta bada umarnin a koma makaranta, kada su koma bakin aiki sakamakon kin aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 da kuma wasu hakokkin su da suka dade a jingine.
Domin karin bayani saurari rahoton Halima Abdulra’uf.
Your browser doesn’t support HTML5