Malaman Addinin Musulunci Sun Yi Kira Ga ‘Yan Siyasa Su Kiyaye Laffuzan Su Yayin Neman Zabe

Taron Malaman addinin Musulinci a Najeriya

Malaman addinin Musulinci a Najeriya na amfani da tarukan Maulidin Annabi Muhammadu (SAW) dake gudana a garuruwan kasar wajen kiraye-kiraye ga ‘yan siyasar kasar su kiyaye laffuzan su yayin gudanar da gangamin neman kuri’a, tare da jaddada muhimmancin cika alkawari bayan samun nasarar zabe.  

A wannan wata na Rabiul Auwal ne al’umar musulmi a sassan duniya, musamman mabiya darikar Tijjaniya a yankin nahiyar Afrika ta yamma ke gudanar da tarukan lakcar maulidi, inda ake tanbihi kan tarihin ranar haihuwa da salon rayuwar Annabi Muhammad.

Kusan shekaru 80 kenan aka kwashe ana gudanar da taron maulidi a makarantar marigayi Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare-Bari, g daya daga cikin mashahuran addinin Islama a Kano.

Taron Mauludi

Khalifa Bashir Tijjani Usman Zangon Bare-Bari jagoran aikace-aikacen wannan makaranta dake zaman cibiyar harkokin ilimin Islama a tafarkin darikar Tijjaniya kuma a karkashin kulawar sa ne ake gudanar da taron Maulidi na wannan cibiya a kowace shekara, yace daya daga cikin manufar taron maulidi ita ce bayyana halaye da dabi’un Manzon Allah domin bayin Allah suyi koyi da shi.

KHALIFA BASHIR TIJJANI USMAN ZANGON BARE-BARI KANO

A nashi bayanin, limaman babban masallacin Juma’a na Murtala a Kano, Malam Kabiru Dantaura, tsokaci yayi game da sarkakiyar dake tattare da alkawari, la’akari da yadda ‘yan siyasa ke yiwa ‘yan kasa alkawura a yayin gangamin neman kuri’a, yace yana daga cikin koyi da manzon Allah mutane suyi alkawari kuma su cika . Ya kuma bayyana cewa, akwai hadari ga rayuwar masu daukar alkawari a kowane mataki kuma su karya.

Wani muhimmin al’amari shine laffuzan da ‘yan siyasar kan furta wajen tallata ‘yan takara ko jam’iyyun su.

Khalifa Bashir Tijjani Zangon Bare-Bari ya yi nasiha, yana mai cewa, tilas ne mutane su kiyaye harshen su domin gujewa halaka ko kawo yamusti a tsakanin al’uma.

Tun a juma’ar da ta gabata ne, gwamnatin Najeriya ta kebe yau litinin a matsayin ranar hutu ga ma’aikata a wani bangare na zagayowar haihuwar Annabi Muhammad S.AW.

Baki daga kasashen Kamaru da Jamhuriya Nijar da Burkina-Faso da kuma Mali da sauran kasashen Afrika ta Yamma na halartar tarukan Maulidi a Kano da sauran garuruwa a Najeriya.

Saurare rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Malaman Addinin Musulinci Sun Yi Kira Gay An ‘Yan Siyasa Da Su Kiyaye Laffuzan Su Yayin Neman Zabe