A duk shekara Majalisar Dinkin Duniya ta ware rana ta yau, 21 ga watan Satumba a matsayin ranar fadakar da al'umma kan mahimmancin zaman lafiya.Taken na wannan shekara shine "hakkin zaman lafiya shekaru 70 da aka ayyana hakkokin bil'adama a duniya."
Dr Ahmad Gumi, malamin addinin Musulunci yayi bayani kan yadda za a shawo matsalolin kasar, inda yace dole a samo canjin tsarin yadda ake gudanar da lamura a kasar a siyasance, a kowanne yanki kuma dole a sanya mutane a ciki.
Pasto Yohanna ma ya bada tasa gudunmawar, inda yace hakan zai kawo karin fahimta tsakanin mabanbanta addinai kabilu ko bangarori da Allah ya kaddara zasu zauna tare. Ya kara da kira ga mutanen Najeriya na kowanne addini da su fahimci juna su kuma zauna lafiya.
Ga Alphonsus Okoroigwe da rahoto...
Your browser doesn’t support HTML5